Rahoton da aka yi wa taken: “Kimar Aiki nan gaba a Ghana: Hanyoyi zuwa ga Ayyuka masu Dorewa, shawarar yin cikakken tsari don cike gibin da ke tsakanin guraben aikin yi na yau da kullum da kuma bunkasa kasuwar aiki”, ya kara da cewa, kashi 75% na ma’aikatan Ghana na fannin masu zaman kansu ne dake kunshe da sana’oi masu kanana da matsakaitan jari.
A wajen kaddamar da rahoton, shugabar hukumar UNDP a Ghana, Angela Lusigi, ta jaddada muhimmancin gina dan Adam ta hanyar ilimi, samar da ababen more rayuwa, da fasaha don samar da ayyukan yi masu dorewa, musamman ga matasa. Ta kara da cewa:“Idan ana duban makomar aiki, to tilas ne a duba tasirin masu basira da hazaka, kuma tilas ne a duba ababen more rayuwa da za su tallafawa masu harkokin kasuwanci, da kananan sana’o’in da ke bukatar bunkasa da kuma kirkiro ayyukan yi. Tace, rashin aikin yi ga matasa wani bam ne da zai iya tashi ko wane lokaci, don haka akwai bukatar mu dauki matakin gaggawa don magance matsalar.”
Kalubalen rashin aikin yi ga matasan Ghana na matukar tasiri ga tunaninsu da karayar gwuiwa wurin neman ilimi, kamar yadda wata matashiya da ta kammala jami’a shekaru shida da suka gabata amma ba ta samu aikin yi ba ta bayyana. Tace, “Ta yaya wadanda suke bayanka za su samu kwazon zuwa makaranta? Ba za su je ba, saboda wadanda suke gabansu ma sun je makarantar, amma suna gida ba su kulla komai ba.”
A hirar shi da Muryar Amurka, masani kuma mai sharhi kan harkokin tattalin arziki, Hamza Attijjany yace, rashin aikin yi ga matasa babbar barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban kasa. Don haka, ya kamata gwamnati ta, “mayar da hankali wurin baiwa matasa ilimin fasaha da kimiya, yadda za su iya dogaro da kan su idan sun kammala karatu, ba lallai sai sun yi dogaro da gwamnati ba”.
Hamza Attijjany ya kara da cewa, ya kamata gwamnati ta kara dankon alaka da kamfanoni masu zaman kan su, ta hanyar sauwaka musu wasu harajoji da yanayi mai kyau na gudanar da ayyukansu, don bincike ya nuna cewa, mafi yawancin matasa na aiki a ire-iren wadannan kamfanoni ne.
Sakamakon bincike da shawarwarin rahoton, ya bayar da taswirar sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arzikin Ghana, wanda aiwatar da shi zai bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki, da suka hada da gwamnati, da kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin farar hula, da kuma daidaikun mutane.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah:
Dandalin Mu Tattauna