A Jihar Katsina, wata mace mai suna Karima Usman, ‘yar shekara 38 da haihuwa, tana zagayawa gida gida, unguwa unguwa a gundumar Yamma, don shawo kan iyaye su amince da wannan maganin. Ma’aikatan lafiya da yawa suka ce ganin halin da take ciki, da kuma irin bayanai da kalamun da take yi ma iyaye, wasu da dama da suka ki karbar maganin tana samun nasarar shawo kansu.
Malama Karima ta kamu da cutar shan inna tun tana ‘yar shekara 3 da haihuwa, kuma ta ce a lokacin da take jaririya, ba a bi giuda-gida ana bayar da wannan maganin. Ta ce ta shiga wannan aikin watanni uku da suka shige, kuma ba zata har sai dukkan iyaye sun yarda a ba ‘ya’yansu maganin.
Shi ma Auwal Bawa, dan shekara 30 da haihuwa kuma mai fama da cutar Polio, yana zagayawa a wani bangaren na Jihar Katsina, domin gudanar da ayyukan horaswa, tattaunawa da jama’ar unguwanni da makamantansu a kan muhimmancin karbar maganin rigakafin Polio.
Haka a Jihar Sokoto ma, daya daga cikin jihohin da ake fama da masu kin karbar maganin, wata gurguwar da ta kamu da wannan cuta, Fatima Aliyu, ta kan bi gida-gida don tabbatar da cewa an yi ma yara rigakafi. Ta ce ya kamata iyaye su daina jin rade-radin karya, domin ita kanta ba zata fito ta bar ‘ya;yanta biyu a gida domin goyon bayan abinda ta san zai cutar ba.
Babbar jami’ar sadarwa ta yaki da cutar Polio a ofishin UNICEF na Najeriya, Melissa Corkum, ta ce wadannan guragu masu fama da cutar, sun a taimakawa gaya a yakin da ake yi da wannan cuta, domin su kan iya shawo kan kasha 70 cikin 100 na iyaye su karbi wannan maganin.