Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Tilastawa ‘Yan Gudun Hijira Komawa Gidajensu Ba - Zulum


Wasu 'yan gudun hijira a jihar Bornon Najeriya (Facebook/ Borno Government)
Wasu 'yan gudun hijira a jihar Bornon Najeriya (Facebook/ Borno Government)

Dubban mutane ne ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da ke kananan hukumomin Kukawa, Marte, Bama, Gwoza da Ngala.

Gwamnatin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ta ce za ta ba ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu zabin komawa gidajensu na asali.

Gwamna Farfsesa Babaga Umaru Zulum ne ya bayyan hakan yayin da aka fara shirye-shiryen mayar da ‘yan gudun hijirar gidajensu na asali a yankunan da aka samu zaman lafiya.

Dubban mutane ne ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da ke kananan hukumomin Kukawa, Marte, Bama, Gwoza da kuma Ngala.

Sun kwashe akalla shekara bakwai rabonsu da gidajensu da suka baro sanadiyyar rikicin Boko Haram.

“Gwamna Zulum ya ce ba za a tilastawa kowa ya bar inda yake ba, sannan gwamnati za ta tallafawa wadanda suke da burin su koma gidajensu, da guzuri domin su sami sauki fara sabuwar rayuwa.” Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce.

A cewar Zulum, yanayin rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira na da matukar wuya yayin da ake fuskantar matsaloli na aikata manyan laifuka.

XS
SM
MD
LG