Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira Sun Ce Sun Fi Bukatar a Samar Masu Tsaro Su Koma Gidajensu


Gwanatin jihar Nejan Nigeria ta kai kayan tallafin kayan abinci ga wasu daruruwan yan gudun hijira wadanda suka tsere daga garuruwansu a sakamakon hare haren yan bindiga da suka addabi wasu yankuna na jihar Nejan.

To sai dai ‘yan gudun hijirar da suka fito daga kananan hukumomin Shiroro da Muya sun ce sun fi bukatar samar masu da tsaro ta yadda zasu koma su debe amfanin gonarsu.

Alh. Ibrahim Inga shine shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar ya ce kayan abincin da suka kai wa 'yan gudun hijirar sun hada da shinkafa masara da taliya da sauransu.

'Yan gudun hijirar dai wadanda ke sansanin 'yan gudun hijira na garin Gwada sun ce sun ji dadin tallafin da gwamnatin jihar Nejan ta kai masu, amma gaskiyar lamari suna cikin tashin hankali domin kuwa amfanin gonarsu na daji.

Yankin na Shiroro da Muya dai ya dade yana fama da hare haren yan bindigar da Gwamnatin Jihar Nejan tace mayaka ne na kungiyar boko haram.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


XS
SM
MD
LG