Rundunar sojojin kasar Kamaru da kuma na rundunar taron dangi da ake kira Alpha, sun sauya salon yaki da yan Boko Haram a cikin kasar, daga yankin kwalfata dake arewacin kasar, har zuwa kan iyakarta da Najeriya.
Yanzu dakarun sun fara shiga kauye kauye suna bin 'yan binidgar a wurare da suke buya. Wakilin Sashen Hausa Awwal Garba, wanda ya aiko da wannan rahoto, yace ta kai dakarun sun shiga kona kauyukan da 'yan bindigar suka buya.Sai dai bai yi bayani kan makommar mazauna kauyukan wadanda ba 'yan Boko Haram ba.
Wani kwamandan rundunar taron dangi ta Alpha, yayi jawabi ga 'yan kunigyar kato da kora, inda ya basu tabbacin hadin kai da goyon baya a ci gaba da yunkunrin ganin an kawar da 'yan kunigyar Boko Haram ko ina suke a jamhuriyar kamaru.
A martaninsa, shugaban 'yan kato da goran, yayi alkawarin zasu yi aiki kafada-da kafada da dakarun wajen samun nasara kan 'yan binidgar.
Ga karin bayani.