Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an tsaro sun kunce wani bam a tsakiyar Maidugurin jihar Borno


Gwamnan jihar Borno Shettima
Gwamnan jihar Borno Shettima

Allah ya kiyaye bam din da aka ajiye a wata babbar hanya dake tsakiyar birnin Maiduguri inda mutane ke hada hada bai tashi ba.

Jami'an tsaro sun gano wani bam da aka ajiye a tsakiyar titin Circula dake tsakiyar birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Da misalin karfe daya na rana yau kaa gano bam din. Ana kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka ajiye shi. Titin dai na cike da shaguna inda mutane ke hada hada.

Jami'an tsaro sun kori duk wadanda suke wurin kafin su kunce bam din wanda kuma an yi lami lafiya ba tare da taba kowa ba. Wurin dai kewaye yake da jama'a to amma abun mamaki ne yadda har aka ajiye bam din a wurin.

Wai wani soja ne da ya zo sayen abinci ya lura da abun ya kuma fadawa mutane bam ne kowa ya bar wurin. Bayan da jami.an tsaro suka isa wurin suka rage karfin bam din sun tadashi inda aka ce yayi wata kara da ba'a taba jin irinta ba.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG