Bayan wata ganawa jiya Laraba, ministocin sun fitar da sanarwa inda suka jadada cewa, warware rikin siyasar kasar Syria ita kadai ce mafita a tashin hankalin da ake fama da shi a kasar.
Sun kuma bayyana goyon bayan abinda suka kira muhimmin ci gaba a yunkurin raba Syria da makamai masu guba.
Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry da kuma babbar jami'ar harkokin kashen ketare na KTT Catherine Ashton sun yi tasu ganawar domin tattaunawa kan taron wanzar da zaman lafiyan da za a gudanar da nufin kafa gwamnatin hadin guiwa a Syria.
Gwamnatin kasar Syria da kuma babban kungiyar kawancen 'yan hamayya dake kin jinin shugaba Bashar al-Assad sun ce zasu halarci taron, sai dai babu tabbacin sauran wadanda zasu halarta.
Jiya Laraba a Syria, harbin roka da aka yi a unguwannin dake karkashin ikon gwamnatin kasar ya kashe a kalla mutane 17. Kungiyar kare hakin bil'adama ta kasar Syria dake zaune a Birtaniya tace farin kaya da kuma sojoji suna daga cikin wadanda suka rasu.
Aleppo na daya daga cikin wuraren da fadan yafi zafi a yakin basasan tunda 'yan tawaye suka kwace ikon birnin shekarar da ta wuce.