Ya gayawa jiridar ta kasar Britania cewa gwamnatin Syrian zata bada shawarar kawo karshen barin wasu kasashen ketare suna saka baki, da kuma shawarar fara gina tsarin siyasa na zaman lafiya, a tattaunawar da za’a yi a birnin Geneva, wanda aka dade da dakatar da shi.
Kasar Amurka da Rasha sun share watanni suna kokarin hade kan gwamnatin Syria da dakarun Tawaye a abinda aka kira “Geneva Two talks.”
A karon farko na wannan tattaunawa, ba’a cimma komai ba, saboda babu wanda ya wakilci duka sassan biyu. Masu adawan na Syria da kawunansu a rabe yake, sun ki hallartar tattaunawar wai har sai shugaba Bashar al-Assad yayi murabus.
Yunkurin kasa da kasa wajen kawo masalaha irin ta siyasa a rigingimu ya farfado bayan dai-daituwa da Amurka ta cimma da Rasha, akan Mr. Assad ya rabu da makamansa masu guba.
Kafin a yanke wannan shawara, Amurka tayi barazanar kai hare-haren soji domin ladabtar da gwamnatin Syria, saboda ance tayi amfani da makamai masu guba da suka kashe daruruwan mutane a wata unguwa dake kusa da birnin Damascus, wanda ke karkashin ikon masu tawaye a watan da ya wuce.