Parfessa Bube Namaiwa na jami'ar Anta-Diouf dake Senegal yace akwai alamun Majalisar zata fi maida hankali kan matakan sulhu a rikici iri daban daban da ake fama da su a fadin duniya.
Haka kuma shehin malamin ya yi magana kan kotun kasa da kasa da yadda tuhumar da ta yiwa shugaba Umar al-Bashir na Sudan ta janyo tankiya kan ziyarar da shugaban na Sudan yake so yayi zuwa New York domin ya halarci taron majalisar Dinkin Duniya, Amurka kuma tana sanyin jiki wajen bashi damar zuwa nan.