Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afrika Sun Ji A Jikinsu Kan Bukatar Zaman Lafiya Da Wadata: Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kasashen Afrika duka sunjii a jikinsu game da batun zaman lafiya da wadata.

Shugaba Muhammadu Buhari yace lokaci yayi da shugabannin kasashen nahiyar Afrika zasu zage damtse domin cimma manufa baya. Da yake amsa tambaya game da yadda kasashen nahiyar Afrika zasu iya aiwatar da muradun karni da Majalisar Dinkin Duniya ta sa gaba sai yace, fatar kowacce gwamnati ko da wacce jam’iya take, ita ce ganin an sami zaman lafiya, kuma an samarwa al’umma aikin yi. Inda al’ummazasu iya noma binda zasu ci kuma har su sayar a kasashen duniya.

Shugaba Buhari yace abubuwa da suke da muhimmanci ga ci gaban al’umma sun hada da tabbatar da tsaro da samar da wutar lantarki, da hanyoyi masu kyau, da ruwan sha, da makarantu da kuma asibitai. Yace wadannan sune burin kowacce gwamnati musamman kasashe masu tasowa.

A cikin hira da Muryar Amurka wajen taron kolin Majalisar Dinkin Duniya, shugaba Buhari yace an riga an tserewa kasashen Afrika, kasancewa mayan kasashen duniya sunfi Afrika ilimin zamani da ci gaba a fannin kimiyya da fasaha, da yawan ma’aikatu da guraban ayyukan yi, da fannin iya dogaro ga kai. Banda haka kuma kasashen da suka ci gaba sun samar da dukan ababan jin dadin rayuwa da suke samar da yanayin samun zaman lafiya.

Dangane kuma da batun Boko Haram shugaba Buhari ya bayyana cewa, ba a sanar da Najeriya ba a wani taron da aka shirya domin kasashen tafkin Chadi da aka gudanar kan harkokin tsaro. Yace, ya ziyarci kasashe da dama cikin mako guda da hawansa karagar mulki inda ya gana da shugabannin kasashen duniya kan batun tsaro da nufin cimma matsaya kan yadda za a tunkarii harkokin tsaro a wannan yankin.

Ga cikakkiyar hirarsu da Mahmood Lalo.

Hira da Shugaba Buhari a Taron Majalisar Dinkin Duniya-3:38"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG