An shiga rana ta 2 yau a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda kasashen duniya ke cigaba da gabatar da jawabai da kuma bayyana ra’ayoyinsu kan muhimman batutuwa. Kamar yadda mai masaukin baki Amurka da Najeriya su ka gabatar da na su jawaban jiya, yau Kasashen Kamaru da Cadi ne ke gabatar da nasu.
Abokin aikinmu da ya je Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniyar da ke birnin New York na Amurka , Mahmud Lalo, ya gaya ma abokiyar aikinmu Maryam Dauda cewa baya ga muhawarar da ake yi a Majalisar akwai kuma wasu muhimman batutuwan da ake ta tattaunawa akansu a bayan fage. Batutuwan bayan fagen sun kuma hada da na tattalin arziki da canjin yanayi da ta’addanci ko tsattsauran ra’ayi da dai sauransu. Hasalima, in ji Mahmud, Buhari na halartar taron da ya shafi ta’addanci n da sauransu.
Da Maryam ta tambaye shi bambancin muradu 8 da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana masu suna MDG a takaice da kuma wadannan na yanzu da ake kira SDGs, da ake ta tattaunawa akai, sai Mahmud ya ce muradun yanzu guda 17 da na baya sun banbanta ta fuskar adadi, kuma 17 din dori ne kan 8 da su ka gabata. Sannan yayin da na baya 8 din su ka fi karkata ga kasashe masu tasowa, su guda 17 din kuwa sun shafi daukacin duniya saboda ganin an dan warware matsalolin da su ka gabata. To saidai Mahmud ya ce akwai nasaba tsakanin muradun baya da na yanzu ta bangarorin daban-daban, hasalima, wasu daga cikin muradu 17 su na kuma cikin 8 da su ka gabata.
Da ya ke amsa wata tambayar kuma, Mahmud ya ce an lura cewa kasashe sun cimma nasarori dabandaban akan mabanbantan muradu saboda banbancin yanayinsu da karfinsu da kuma abubuwan da su ka fi bukata.