Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Akan Ta'addanci a Najeriya


Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Buhari ya ce irin wanda mutane ne suka hadu da ‘yan Boko Haram.

Da yake jawabi kan ta’addanci a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce duk mun san yadda ‘yan Boko Haram suka faro da akidar su mun kuma san yadda ‘yan tsageran gani kasheni na Niger Delta, suka fara su masu yiwa tattalin arzikin Najeriya, zagon kasa ne inda suke lalata bututun Man fetur da na iskar gas da sauransu.

Amma a arewacin Najeriya, kuwa yaki ne da ‘yan ta’adda, muraran, abun da ya faru a LIbiya da abun da yake faruwa a Mali, yasa mutane da suka samu horaswa akan iya sarrafa makamai suka samu kan su a Tafkin Chadi, wanda ya hada kasashen Najeriya, Kamaru, Chadi da jamhuriyar Nijar.

Shugaba Buhari, ya ce irin wanda mutane ne suka hadu da ‘yan Boko Haram suna kaiwa mutane hari, yana mai cewa babu wata kasar da zata iya bada tabbacin cewa ba za’a iya kai mata hari ba ta kowace irin fuska.

Ya kara da cewa Amurka, ta dauki mahimmin mataki na ganin cewa ta taimaka wajen bada bayanan siri na gano duk inda ‘yan ta’adda suke domin tarwatsa su.

XS
SM
MD
LG