Batutuwan da aka fi maida hankali a zauren Majalisar su ne “Dawwamammun Muradun Raya Kasashen” nan guda 17, wadanda ake so a cimma nan da shekarar 2030.
A daren jiya ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa a gaban Majalisar.
Daga birin New York da ke nan Amurka, ga rahoton da Mahmud Lalo ya aiko mana.
REPORT: Yadda aka gabatar da shugaban Najeriya ke nan Muhammadu Buhari a gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya, yayin da zai isar da sakonsa a gaban Majalisar.
Shugaban Najeriya ya fara magana ne akan Dawammamun Muradun Raya Kasashen da aka shata guda 17, wadanda ya kwatantasu kamar haka……….
Ya ce yadda aka shata wadannan muradu sun zo da ababan kwadaitarwa, idan ka kyale ni zan iya ce abubuwa ne da ke da tushe. Amma idan har ana so a cimmawadannan muradu su yi tasiri a duniya, dole ne sai an dauki matakan aiwatar da su.
Shugaban Najeriya, bai gaza wajen bayyanawa zauren Majalisar babban abinda ya ke ciwa kasar tuwo a kwarya ba……
Ya ce “amma a yanzu, matsalar ta’addanci ita ce abin da ke bukatar kulawa. Yanzu haka Najeriya da makwabtanta, da suka hada da Kamaru Chadi da Nijar har ma da Jamhuriyar Benin, na aiki kafa da kafada wajen ganin sun shawo kan wannan matsala a karakashin hadaka ta kasashen Tafkin Chadi. Mun hada wata rundunar hadin gwiwa wacce za ta tunkari ta kuma ga bayan kungiyar Boko Haram.”
Wani batu kuma da shugaban na Najeriya ya tabo shi ne wanda ya ja hankulan kasashen duniya da dama, wato batun ‘Yan matan Chibok………
Ya ce “ Shugaban Majalisa, daya daga cikin abin da muka sa a gaba shine mu ga cewa mun kubutar da ‘yan matan Chibok da ransu kuma ba tare da sun samu wata illa ba. Muna aiki dare da rana, domin mu tabbatar da cewa mun kubutar da su, sun koma ga iyayensu. A koda yaushe suna zukatanmu suna kuma cikin jininmu.”
A karshe, Muhammadu Buhari ya kuma tabo batun cin hanci da Rasahawa da ya yiwa kasar katutu…….
Ya ce “ bari na kara jaddada matsayin gwamnatin Najeriya, game da matsalar cin hanci da rashawa. Babu gudu babu ja da baya, wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma yadda ake safarar kudaden haram.
To a yau Talata ne ake sa ran shugaban Najeriya zai kama hanyar komawa gida.
Ga rahoton Mahmud Lalo daga New York nan Amurka inda ake taron.