Zanga zangar da aka yi a Conakry babban birnin kasar Guinea ya halaka mutum daya kwanaki biyu kamin a gudanar da zaben shugaban kasa, wanda 'yan hamayya suke son ganin an dage shi.
Kamar yadda wakilin Muriyar Amurka a kasar yayi bayani, 'yan hamayya sun matsa kaimin ganin an dage zaben, suna zargin hukumar zaben kasar da nuna son kai. Sakamakon zaman dar dar da ake yi aka goce da bore a jiya jumma'a inda 'yan dibar ganima ciki har da jami'an tsaro suka farwa wata kasuwa dake binrin. Haka nan an fuskanci arangama tsakanin magoya bayan jam'iyun siyasar kasar.
Wannan lamari yana aukuwa ne kamin zaben kasar karo na biyu kenan tun bayan da Guinea ta koma bin tafarkin demokuradiyya a 2010. 'Yan takara masu yawane suke neman su kalubalanci shugaban Alpha Conde, inda ake kallon tsohon PM Cellou Dalien Diallo a zaman wanda yafi barazana ga shugaba mai ci.
Ahalinda ake ciki kuma kwamitin sulhu na MDD ya amince da wasu karin matakai da zasu taimakawa rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya dake karkashinta mai karfin sojoji fiyeda dubu 12 a Sudan ta kudu, su kare farar hula sannan su yi matsin lamba kan sassan biyu da basa ga maciji su aiwatar da yarjerjerniyar zaman lafiya da suka kulla ranar 25 ga watan Agusta.
Kwamitin sulhu mai wakilai 15 ya nemi da a kawo karshen tashe tashen hankula nan take, a dai dai lokacinda yarjejeniyar take fuskantar kalubale daga dukkan sassan biyu.