Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Mulkin Sojan Guinea Ta Nada Sabon Firaminista


Amadou Oury Bah
Amadou Oury Bah

Gwamnatin mulkin soja ta Guinea ta fada jiya talata cewa ta nada sabon firaminista kwanaki takwas bayan rusa gwamnatin da ta shude, yayin da harkoki a Conakry, babban birnin kasar su ka tsaya cik a rana ta biyu ta yajin aikin gama gari.

Masu zanga-zangar dai na neman a sako shugaban kungiyar da ake tsare da shi tare da rage farashin kayan abinci da kawo karshen hana 'yan jarida aikinsu da kuma kyautata yanayin rayuwa ga ma’aikatan gwamnati.

An dai kira yajin aikin ne yayin da tashe tashen hankula masu nasaba da yanayin rayuwa ke karuwa, ga kuma rashin gwamnatin rikon kwarya bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta sanar da rusa ta a makon da ya gabata, ba tare da bayar da wasu dalilai ba.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin da yammacin jiya Talata, mai magana da yawun shugaban mulkin soja Janar Mamady Doumbouya ya ce "an nada masanin tattalin arziki Mr Amadou Oury Bah, a matsayin Firayim Minista kuma shugaban gwamnati."

Kakakin ya ce babban aikin Oury Bah shi ne kawo karshen rikicin gwamnati da kungiyoyin kwadago 13 da suka kira yajin aikin da aka fara a ranar litinin, wanda ya yi sanadin harbin mutane biyu a wani fadan da aka rika yi a unguwannin Conakry.

Mai magana da yawun kungiyar Amadou Diallo ya gaya wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa yana jiran “a cike dukkan bukatun” kafin kawo karshen yajin aikin, ya kara da cewa babu wata ganawa da suka shirya da hukumomin kasar a ranar Talata.

Kungiyoyin sun bukaci sakin Sekou Jamal Pendessa, babban sakataren kungiyar kwararrun 'yan jarida ta Guinea (SPPG), a matsayin wani sharadi na duk wata tattaunawa da gwamnatin mulkin soja.

An dai kama Pendessa ne a karshen watan Janairu saboda "gudanar da zanga-zangar ba tare da izini ba" kuma a ranar Juma'a an yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, ko da yake an dakatar da uku daga cikinsu su.

Ba kasafai ake yin zanga-zanga ba a karkashin shugaban mulkin soja Doumbouya, wanda ya karbi mulki a watan Satumba na 2021, an kuma haramta ta a shekarar 2022.

Sojoji sun kame da dama daga cikin shugabannin 'yan adawa da 'yan kungiyoyin farar hula da kuma wakilan manema labarai, yayin da aka ciccire tashoshin talabijin da kuma katse tashoshin rediyo.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG