Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kamaru Da Najeriya Sun Ceto Mutane Daga 'Yan Boko Haram Bayan Barin Wuta


 A Boko Haram fighter lies dead after an attack on Dikwa, Borno State, Nigeria, February 24, 2016.
A Boko Haram fighter lies dead after an attack on Dikwa, Borno State, Nigeria, February 24, 2016.

An fafata tsakanin sojojin kasashen Najeriya da hadin gwiwar na Kamaru wajen kashe 'yan boko haram kusan guda 100 a wani kauyen kan iyakar kasashen biyu.

Kasar Kamaru ta bayyana cewa sojojinta tare da na Najeriya sun ceto daruruwan mutane da ‘yan boko haram suka yi garkuwa dasu, sannan sun kashe fiye da ‘yan ta’addar na Boko Haram kusan 100 a wani samamen da suka kai.

Kwamandojin askarawan sun ce, hakan ta faru ne lokacin da suka yiwa wani gari mai suna Kumahe dirar mikiya akan iyakar Najeriya da Kamaru, a wani shirin ratattakar ‘yan Boko Haram din da suka yiwa garin katutu.

Harin sojin ya share kwanaki 3 ana yinsa kafin samuwar wannan nasarar ta cetar jama’a. ba dai wata hujjar da ta tabbatar da wannan rahoton, abinda ya biyo bayan rahoton jiya na tattaunawar Sojin Amurka da Najeriya don kai mashawartan soji zuwa Maidugurin Najeriya.

Wani jigo a Amurka ya fadawa Muryar Amurka cewa ana nan ana tattauna yiwuwar kai mashawartan sojojin zuwa jihar Borno don bada shawarwarin yakar ‘yan Boko Haram, sai dai yace har yanzu baa kai ga matsaya ba tukunna.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG