Shugaban yace yin hakan zai kara tsumbula talakan Najeriya cikin mawuyacin hali fiye da bakar wahalar da yake ffuskanta a halin yanzu.
Shugaban yace irin matakan tattalin arzikin da aka dauka can baya basu dace da cigaban al'umma ba. Yace karya darajar Nera kwatankwashi ne da kashe Najeriya. Saboda haka masu bukatar a karya darajar Nera sai sun yi aiki matuka kafin ya yadda. Abun da zai fi son sani shi ne yadda karya darajar Nera zai taimakawa talakan kasar.
Wani kwararrare akan tattalin arziki Sani Dutsinma ya yi tsokaci akan furucin shugaban. Yace dabara ce mai inganci saboda bai kamata a ce kasa ta karya darajar kudinta domin komi da aka sani a kasar ya ta'allaka ne akan abubuwan da ake sayowa daga waje. Da zara an karya darajar kudin to farashin komi zai tashi.
Akan kudurin gwamnati ta samar ma wadanda zasu shigo da kayan da zai inganta kasar, Malam Sani yace bata yiwuwa a ce duk wanda yake bukatar kudin waje a bashi tallafi.
Ga karin bayani.