Dangane da fargabar da wasu a Najeriya ke yi akan sake fadawa cikin hare-haren 'yan Boko Haram, Birgediya Janar Rabe Abubakar daraktan labaru na rundunar sojojin Najeriya yace kungiyar bata da karfin kaiwa kowace kasa irin mugun hari na da.
Yace lamari zai tsaya haka kuma nan ba da jimawa ba sojoji zasu gama da sauran wadanda suka rage.Duk inda suka shiga yanzu za'a fatattakesu. Ba zasu samu mafaka ba na dindindin kamar Sambisa.
Kasashen yankin tafkin Chadin sun kafa wata rundunar soji ta hadin gwuiwa da nufin yakar 'yan ta'adan saidai mutane na ganin rundunar bata kazar kazar.
Kakakin rundunar dake kasar Chadi Kanar Muhammad Dole yace masu shakkar rundunar basu san abun dake faruwa ba ne domin kullum suna kashe 'yan kungiyar tare da kama wasu. Suna nan suna aikinsu suna kuma samun nasara a sintirin da su keyi kan iyakokin kasashen. Suna neman 'yan kungiyar su gama dasu.
Wani kwamandan sojojin sama Tijjani Gamawa yace a matsayinsu na masana tsaro basa wani fargaba saboda kayan aiki da sojojin Najeriya suke dashi da horon da suka samu zai yi wuya a ce Boko Haram zata dawo ta kwace garuruwa kamar da.
Ga karin bayani.