Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Amince Da Kasafin Kudin Bana


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Ga dukkan alamau an kawo karshen takaddama da kuma jita-jita game da makomar kasafin kudin Najeriya na wannan shekarar, bayan da Kwamitin Kudi na Majalisar ya tabbatar da shiga zango na karshe na tabbatar da shi.

Bayan ta yi ta muhawarar da ta kai ga cece-kuce, tare kuma da abin da ta kira la’akari da abubuwan da su ke na zahiri, Majalisar Dattawan Najeriya, musamman ma ta wajen Kwamitinta na Kasafin Kudi, ta amince da kasafin kudin bana.

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Sanata Danjuma Goje ya ce Kamitin ya lura cewa ba za a samu matsalar samun gudin aiwatar da kasafin kudin ba. Ya ce zuwa 27 ga watan gobe za a mika ma Shugaban kasa kasafin kudin don sanya hannu.

Ya ce tun daga yau Alhamis Ma’aikatu za su zo su kare kasafinsu gaban Kwamitin Kasafin Kudin na Majalisar. Ya ce saboda a hanzarta tare kuma da saukaka aki, an maida dukkannin kwamitocin Majalisar sun zama kwamitocin kudi don sauraron ma’aikatu daban-daban masu alaka da su. Ya ce wadannan kwamitocin ne za su kai ma ainihin kwamitin kudi sakamakon sauraron ma’aikatun.

Ga wakiliyarmu Madina Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG