Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin ‘Yan Najeriya Na Rungumar Sufurin Jirgin Kasa Yayin Da Kudin Shigarsa Ya Haura Zuwa Kaso 53% - NBS


Sabon Layin Jirgin Kasa Na Abuja
Sabon Layin Jirgin Kasa Na Abuja

Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ce ta bayyana wadannan alkaluma a rahoton da ta fitar a jiya Alhamis.

‘Yan Najeriya da dama sun fara rungumar tsarin sufurin jiragen kasa yayin da kudin shigar bangaren ya karu zuwa Naira biliyan 1 da miliyan 690 a zango na 2 na shekarar 2024 da muke ciki, abinda ya nuna samun karuwar kaso 53. 14 cikin 100 idan aka kwatanta da naira biliyan 1 da miliyan 100 da aka samu a irin wannan lokaci a bara.

A bara, hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta tara naira biliyan 1 da miliyan 70 a matsayin kudin shigar da ta samu daga fasinjoji.

A cewar rahoton, jumlar fasinjoji dubu 689 da 263 ne suka yi balaguro ta jirgin kasa a zangon na 2 na shekarar, inda aka samu karuwar kaso 45. 38 cikin 100 idan aka kwatanta da fasinjoji dubu 474 da 117 da aka samu a irin wannan zango a 2023.

Haka kuma adadin kayan da aka yi safararsu ta jirgin kasa sun karu matuka, inda aka yi jigilar tan dubu 143 da 759 a zango na shekarar da muke ciki, abinda ya haura daga tan dubu 56 da 936 da aka gani a irin wannan zango a 2023.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG