Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Sama Da Kashi 50 Na kudin Haya Na Barazana Ga 'Yan Najeriya


Newly-built houses on the bank of the River Kaduna are seen in flood waters after hours of rainfall in Kaduna, Nigeria August 15, 2015.
Newly-built houses on the bank of the River Kaduna are seen in flood waters after hours of rainfall in Kaduna, Nigeria August 15, 2015.

Masu haya a manyan biranen Najeriya kamar Abuja, Legas, da Fatakwal, na kokawa a kan yawan karin kudin haya daga kaso 50 zuwa sama da masu gidajen haya ke yi ba tare da la’akari da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a kasar ba.

Wannan dai wata babbar matsala ce da wadanda ke zaune a gidajen haya ke fuskanta a manyan birane kamar Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, Legas da ke zama tsohon babban birnin kasar, Fatakwal, Katsina da dai sauransu, ke fuskanta inda masu gidajen ke cin karensu ba babbaka a wajen kara kudin haya duk lokacin da suka ga dama.

Lamarin dai a cewar masu hayar na ci musu tuwo a kwarya saboda a mafi yawan lokuta ba su da zabi idan ba su biya kudin da aka yi musu kari ba sai dai su fara neman sabon gida baya ga wahalar da suka sha a baya wajen samun gidan da aka yi karin.

Rukunin gidajen da al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Su ka Bada Tallafi ga ;Yan Gudun Hijira
Rukunin gidajen da al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Su ka Bada Tallafi ga ;Yan Gudun Hijira

A yayin bayyana nasu korafin, wasu mazauna birnin tarayya Abuja sun shaida wa Muryar Amurka cewa, kamata ya yi gwamnati ta sanya ido a kan lamarin na masu bada gidan haya, don a saukake wa jama’a da ke fama da matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa.

Yawaita kari a kudin haya a manyan biranen Najeriya ba wani sabon abu bane, inda a watan Agustan shekarar 2022 sai da wasu mazauna biranen tarayya Abuja suka gudanar da wani tattaki, don neman gwamnati ta shiga cikin lamarin karin da ake yi don agazawa talakawa da ke zaune a wajen gari da ake yawaita yiwa kari duk da cewa ba karin albashi ake yi musu ba.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG