Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Magana Mai Labari Tsoho


Dr. Abdullahi Garba Imam
Dr. Abdullahi Garba Imam

Shirin Harshe da Karin Magana na wannan makon zai yi duba ne akan karin magana mai bada labari, wato karin maganar da ya kunshi labari.

A makon daya gabata ne Dakta Abdullahi Garba Imam, yayi mana bayanin karin magana mai sana’a, amma wannan satin zai tashi ne da karin magana mai labari. Inda yace shi wannan karin maganar mai labari shine irin karin maganar da mutum ba zai sanshi ba har sai mutum ya san asalin sa, kasancewar karin magana ne da fadar sa ake kawai amma ba kowa ne ya san asalinsa ba, kuma sai an san asalin sa domin ta nan ne mutum zai gane me ake nufi.

Shi dai wannan karin magana ya kasu kashi biyu, kamar yadda manazarta suka rarraba shi, na farko dai shine karin magana mai labari tsoho, na biyu kuwa shine karin magana mai labari sabo, amma baki ‘dayansu ba za’a iya cewa ga adadin su ba.

Karin magana mai labari tsoho, wannan kuwa ya danganta da garuruwa ko kasa ko nahiyar da mutane suke, domin ya danganta da inda mutane suke kasancewar kowa na amfani da irin nasu. Missali ga ‘daya da ya shahara ‘Fadan Goggo A Kofa’ wannan karin maganar na nunin sai kasan labarin Goggo kafin kasan me ake nufi, ga duk wanda yasan labarin to zai san cewa ita Goggo yara sunyi mata laifi a birni, amma lokacin da ta dawo Kofa kuma yara sunayi mata sannu da zuwa sai ta hausu da fada, to inda akayiwa Goggo laifi ba a nan tayi fada ba.

Saurari Dakta Abdullahi Garba Imam domin jin cikakken bayanin karin magana mai labari.

XS
SM
MD
LG