Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniyar Fina Finai Tare Da Hussaini Danko


Hussaini Abubakar
Hussaini Abubakar

Shirin duniyar Fina Finai na wannan makon Dandali ya sami bakuncin mawaki Hussaini Abubakar, wanda akafi sani da Hussaini Danko wanda yace a iya rayuwar sa dai Allah ya cika masa burinsa.

Hussaini dai ya bayyana mana yadda yafi wayo a harkar wake-wake da kade-kade irin na Hausa, wakokin da yake yi dai sun hada da wakokin Fim na Hausa da na siyasa harma da ta biki dama suna.

Wakar ‘Basaja’ itace dai kamar bakandamiyar Hussaini domin da ita aka fi sanin shi a duniya, wakar dai zata kai kamar shekaru hudu da yinta kenan. Abin da kuwa ya janyo hankalinsa har ya fara rera waka shine, ya taso tun yana yaro da sha’awar harkar wake-wake, Allah kuma ya sa yayi wayo gashi yanzu ya tsinci kansa cikin wannan sana’a.

Shekaru shida kenan tun da Hussaini ya fara harkar rera wakokin Hausa, duk da yake baiyi nisa a zangon karatun sa ba amma yana da niyyar komawa makaranta nan bada dadewa ba. Hussaini ya samu lambar yabo cikin wakokin sa da dama da suka fito wasu fina finai.

XS
SM
MD
LG