Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Louis van Gaal, yayi biris da sukar da wani tsohon dan wasansa, Hristo Stoichkov, yayi masa da kakkausar harshe cikin wannan makon a kafofin yada labarai na kasar Spain.
Stoichkov dan kasar Bulgariya, wanda aka sani da kaifin harshe, ya bayyana van Gaal a zaman manajan da bai iya koyar da wasa na kirki ba, tare da zarginsa da laifin wargaza duk wata kungiyar da yayi jagorancinta. Van Gaal da Stoichkov sun bata a lokacin da dukkansu suke tare da kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona.
Van Gaal yace a duk lokacin da ya ji wata magana, yak an fara da nazarin shin wanene yake fadin maganar, domin ya san dalilin da ya sa wannan mutumin ke fdadin abinda yake fada. Yace, “wannan bai dame nib a a saboda a matsayi nan a manaja, akwai abubuwa da dama da na zartas, kuma Stoichkov yana cikin wadanda na kora, abinda yasa yake wannan babatun ke nan.” In ji Van Gaal.
Suna iya fadin abinda duk suke son fada, amma ba koyaushe ne suke fadin gaskiya ba, musamman a wannan sha’ani na kwallon kafa.
Van Gaal yace ya saba da jin irin wannan suka, don ba yau aka fara yi masa ba, Luka Toni ma ya sha sukarsa. Amma kuma ‘yan wasan dake yaba mini sun ninka mutane irinsu Stoichkov da Toni nesa ba kusa ba