Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawancin Mutane Na Mana Kallon ‘Yan Bariki – inji Ali Artwork


Ali Artwork
Ali Artwork

Dandalin Voa ya sami zantawa da Aliyu Mohammad Idris, wanda akafi sani da Ali Artwork shi dai edita ne masana’antar fina finai, wanda ya bayyana mana abin da ya janyo hankalinsa ga harkar fina finai.

Sana’a goma maganin mai gasa, Shi dai Ali edita ne kuma mai bada umarni ga shi kuma jarumin fina finai, yace abinda ya janyo hankalinsa ga harkar fina finai shine wannan harka ce da za’a iya aikawa da sakonni ga mutane da dama, sannan mutum kuma zai ma iya taimakawa addini a cikin wannan harka.

Harkar fim dai sana’a ce a wannan zamani idan aka duba yadda yawan mutanen da ke harkar sun kai kimanin dubu goma zuwa ashirin, wadanda sana’arsu kenan kuma mafi yawancin su matasa ne.

Ali Artwork dai yace yawancin mutane na yi musu kallon kamar suna harkar barikanci ne a sana’ar tasu, duk da yake wannan fahimta ce ta bai bai tunda ba haka lamarin yake ba, amma da mutanen da suke musu irin wannan kallon zasu dubu yadda masana’antar ke gudanar da lamarin zasu ga cewa ta saba yadda suke kallon ta, domin zasu ga mutane kowa da aikin da yake yi wasu kuma kowa da bangaren da yafi kwarewa.

Burin matashin dai shine nan gaba ya zamanto wani babban mai bada umarni, inda wakiliyar Dandali Baraka ta tambayeshi meyasa baya son zama babban Jarumi? Inda ya fada mata cewa shi yafi son zama mai bada umarni.

XS
SM
MD
LG