Gwamnan jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule yace karancin kudade a kananan hukumomin ne ya sanya ba’a gudanar da zaben ba. Ya bayyana cewa basu biya ma’iakatansu ba ballantana a ce an tara kudin zabe. Da sun ce za’a ci bashi, to a halin yanzu sun kasa samun bashin.
Shima tsohon shugaban kungiyar shugabanin kananan hukumomin Jahar Nassarawa kuma shugaban karamar hukumar Lafiya, Aminu Muazu Maifata ya ce maido da martabar kananan hukumomin ne zai samar da kudaden aiwatar da ayyukan daukacin kananan hukumomin Najeriya.
Tuni dai alummar jahar suka mai da martani cewa gwamnati na son wanda zata juya shi ta inda taso ne shi ya sanya bata gudanar da zabe ba.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: