Masu sauraron mu assalamu alaikum; barkan mu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.
Tambaya 1:
“Don Allah voa hausa ku tambayamin masana: shin mine ne ke janyo matsalar juyin mulki ga kasashenmu na Afirka? Shin ko Akwai wata kasa cikin Afirka da ba a taba yin Juyin mulkin ba”?
Mai Tambaya: Garba Nahali Kamba, Kebbi, Najeriya.
Tambaya 2:
Salamu alaikum, “Don Allah voa hausa, ku tambayamin masana, ko me ke janyo faduwar darajar Naira a Najeriya?
Shin ko me ya sa har yanzu darajar Naira ta ke farfaduwa. Shin laifin gwamnati ne ko 'yan kasuwa?”
Mai Tambaya: Har ila yau, Garba Nahali Kamba, Kebbin Najeriya.
Amsoshi: Bari mu fara da amsar tambaya kan musabbabin yawan juyin mulki a Afurka. Idan Malam Garba Nahali, da ma sauran masu sha’awar ji, na tare da mu, wakilinmu a shiyyar Adamawa da Taraba a Najeriya, Muhd Salisu Lado, ya samo amsa daga Dr Mahdi Abba na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Adamawa, Najeriya.
Sai kuma amsar tambaya kan musabbabin yawan faduwar darajar Naira a Najeriya. Har ila yau dai, idan mai tambayar, Garba Nahali Kamba na tare da mu, wakilinmu a shiyyar Adamawa da Taraba a Najeriya, Muhammad Salisu Lado, ya samo amsa daga Dr Ahmed Tukur Umar na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Adamawa Najeriya.
A sha bayani lafiya:
Dandalin Mu Tattauna