Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanfanin Volkswagen Ya Sa Wa Motocinsa Miliyan 11 Wata Manhaja


Kamfanin Volkswagen na kasar Jamus ya ce, ya sakawa motocinsa miliyan 11 wata manhaja da aka tsara, domin kaucewa gwajin da Amurka ke yi na yawan hayaki da motoci ke fitarwa.

A yau Talata, kamfanin ya bayyana cewa, zai ware biliyan bakwai da miliyan dari uku, domin daukan nauyin sauya wannan manhaja, a wani mataki na sake janyo hankulan kwastomomin kamfanin.

A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya kuma ce yana aiki tukuru domin ganin ya cire wannan manhaja, wacce ta ke ba da damar kaucewa gwajin yawan hayakin na Amurka.

A farkon yinin yau Talata ne, Ministan kudin Faransa, ya yi kira da a gudanar da bincike a nahiyar turai baki daya, kan yadda motoci ke fitar da hayaki, bayan da kamfanin na Volkswagen ya bayyana cewa ya yi zuke, bayan da ya dauki matakan kaucewa gwajin gano cewa motocinsa na fitar da hayakin da ya wuce kima.

Yanzu haka dai hukumin Korea ta Kudu su sun ce za su gudanar da bincike kan motocin na Volkswagen, inda tuni ta gayyaci wakilin kamfanin zuwa birnin Seoul domin su tattaunawa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG