Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Annobar Shaye Shaye Na Ci Gaba Da Barazana


Annobar amfani da kwayoyi da sauran kayayyakin sa maye na ci gaba da barazana ga makomar rayuwar ‘yan Najeriya, musamman Matasa. Kodayake hukumomin na cewa, suna iya bakin kokari domin murkushe mtsalar, amma alkaluman baya-bayan nan, na nuna yadda al’amarin ke kara kazamta, musamman a yankin arewacin kasar.

Masan sun yi bayanai da dama musamman bisa ga irin cututtukan dake da alaka da shan miyagun kwayoyi kamar su ciwon hanta, da sankaran hanta, da ciwon mantuwa da kuma ciwon shanyewar gefen jiki wanda shan giya kan haifar.

Tabar wiwi kuma kamar yadda masana suka bayyana kan haifar da ciwon kwakwalwa da da sauran cututtuka masu alaka da kwakwalwa.

A wata hira da wakilin sashin Hausa ya yi da wasu matasa, sun bayyana dalilan da yasa suke ci gaba da wannan hali na shaye shaye kamar yadda zaku ji.

Saurari rahoton domin karin bayani.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG