Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fita Tare 'Yan Mata Da Samari Shin Burgewa Ne?


A shirin mu na mata a yau mun waiwaye dabi’ar nan na 'yan mata fita zance da samarinsu da kuma zuwa shan Icecream wanda wasu ke ganin hakan shine burgewa.

A cewar wata da mukan zanta da ita, cewa ta yi yan mata masu kwadayi kan bi samarinsu shan icecream da sauran abubuwan shakata daga bisa ni a sauke su a kan hanya kafin a iso gida , su kuma shirga wa iyayensu karyar cewar daga gidan kawayensu suke.

Ita kuwa cewa ta yi burgewa ne kuma passion ne da nuna cewar kana da farin jinni , a ganka a motar saurayinka mai mota mai kyau irinsu hammer jeep domin zuwa hadaddun wuraren shan icecream hakan na nuna kece raini ka dawo ka na taka wa daya bayan daya da leda a hannunka.

A cewarta ba wani kayan gabas ba ne yi wa iyaye alayen cewar daga gidan kawarka ka fito gudun kada a kama karyar ta, ta kara da cewa ko ba komai idan ‘yayan kanninka suka zo,ka ba su kayan kwalama.

Wata kuwa cewa ta yi, ba ta, taba bin saurayin ta shan icecream baa ganinta rashin tarbiyya ne da nuna cewar mace ta isa a cikin sa’anin ta, a zahirin gaskiya cewa ta yi muddin saurayi na kaunarka toh lailai ya kawo ma ko me yake so har gida, domin nuna martabar ka a idonsa.

XS
SM
MD
LG