Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Tunani Na Haddasa Cutar Makanta


Kwa-kwalwar Dan'adam
Kwa-kwalwar Dan'adam

Ashe mantuwa cuta ce? Sauda dama mutane kan dauki mantuwa a matsayin wani abu da yake cikin hallittar dan’adam. Haka yake, amma akwai wata mantuwar da take ta wuce nau’in hallitar dan’adam. Wannan binciken ya tabbatar da cewar, yawaita yawan tunani na haddasa cutar makanta.

Ga ‘yan mata, sau da yawa za’aga mace tana yawan manta wasu abubuwa, da suka kamata ace bata manta da suba. Ko mai ke kawo hakan? An gano cewar kwa-kwalwar mata tana dauke da wasu sunadarai, da suke aiki a kowane lokaci, kuma suna bukatar mace tayi tunani sannu a hankali babu gaggawa, kana sukan sa ma kan su tunanin wasu abubuwa da a lokkuta da dama sunfi karfin su.

A wasu lokkuta mace takan daura ma kwa-kwalwar ta tunanin ya za’ayi ta mallaki wani abu, ko kuma taya zata magance wani abu, wanda duk lokacin da ta shiga wadannan tunanin, sai kwa-kwalwar ta tazama tana aiki sannu a hankali. Musamman ma ldan akace mace tana dauke da juna-biyu, za’a ga cewar har idan ta haihu wannan tunanin bai cika barin taba, domin kuwa a wannan lokacin zata fara sa tunani akan abun da ta haifa. Wadannan suna daga cikin abubuwa da kan haifar ma mata matsalar mantuwa, wadda ba ta da alaka da hallita.

Maza matasa, kan samu matsalar mantuwa, idan suka daukar ma kan su rayuwa shaye-shaye, da rashin nazari kamin aikata abubuwa. Yawan tunani na taimakawa wajen mutun ya samu cutar mantuwa, musamman ma idan matasahi yacika tunani akan wasu abubuwa da suke da wuyar samu a rayuwa. Baki daya akwai bukatar kowane bangare, su guji wadannan abubuwan da kan haifar musu da cutar ta mantuwa, domin kuwa mutane na kara girma, cutar na kara shiga cikin jikin su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG