Ministan watsa labarai a jihar kudu maso yammacin kasar, Ugas Hassan Abdi, yace wasu ‘yan kunar bakin wake su biyu ne suka kai wannan harin yayin da suke saye da damara dauke da abubuwar fashewa. Yace jami’ai na ci gaba da tantance mutane da fashewar ta taba su.
Kungiyar ta’addanci ta al-Shabab mai alaka da al-Qaida, wacce take rike da garin Baidoa tsakanin shekarun 2009 zuwa 2012 kafin dakarun gwamnatin Ethiopia ta koresu daga wurin, ta dauki alhakin kai wannan harin.
Wani da ya sha da kyar, ya fadawa sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, wani dan kunar bakin wake ne ya jefa gurneti a wani wurin cin abinci da jama’a suka taru, ya kashe akalla mutane mutane biyar kuma ya jikata wasu da dama.
Yace matashin ya tinkaro su kuma ya jefa musu gurneti a cikin wurin cin abinci mai cike da jama’a. Yace an dai harbe maharin kafin ya tada bam din jikinsa.
Facebook Forum