Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya Ya Kamu Da Ebola A D.R. Congo


Ma'aikatan Kiwon Lafiya
Ma'aikatan Kiwon Lafiya

Wani ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a gabashin Demokaradiyar Jamhuriyar Congo, ya kamu da cutar ebola a karon farko, tun lokacin da cutar ta barke, a cewar shugaban dakarun kwantar da tarzoma ta MDD.

A cikin wata wasikar da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bankado, shugaban ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a D.R. Congo Leila Zerrougui, tace tana rubuta wannan wasikar domin sanar da babban sakataren Majalisar wani labari mai damuwa, inda aka samu wani abokin aikita a wani sansani a Beni ya kamu da cutar Ebola, wanda a halin yanzu ana kula da jinyarsa.

Zerrougui tace wannan ma’aikaci ya kwashe makwanni bai zuwa aiki, daga nan ne aka fara neman inda yake.

Wannan labarin ya biyo bayan kashedi ne da jami’an kiwon lafiya suka yi a kan yanda sabuwar ebolar take yaduwa cikin gaggawa kuma adadin wadanda suka kamu zai iya ninka abinda aka gani a cikin Satumba.

Ma’aikatar kiwon lafiyar D.R. Congo tace ya zuwa jiya Juma’a wadanda suka mutu sun kai 125, a cikin mutane 201 da suka kamu da kwayar cutar, kana an kuma tabbatar da mutane 166 sun harbu da ma wani karin wasu 35.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yaki Da Matsalar Almajiranci A Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG