Wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya a gabashin Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ya kamu da cutar Ebola, wanda shi ne na farko tun bayan da cutar ta sake bulla a wannan karon, a cewar shugabar tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da zaman lafiya a Kongo.
"Ina mai bakin cikin shaida maku yau cewa mun samu labarin cewa wani abokin aikinmu da ke Beni ya kamu da cutar Ebola kuma yanzu haka ana kan yi masa jinya," a cewar Laila Zerrougui a wata wasikar da ta rubuta, wadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu.
Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an kiwon lafiya ke gargadin cewa yawan yaduwar cutar ta Ebola ya ribanyu har ma da dori tun daga watan Satumba.
Facebook Forum