Katafaren kamfanin harhada magungunan nan na Amurka, Johnson and Johnson, ya dakatar da mataki na karshe na gwaje gwajen maganin COVID-19 dinsa, bayan da aka samu daya daga cikin wadanda ake gwada maganin a kansu, dauke wani irin ciwon da ba a tantance ba.
Wata kafar labaran harkokin lafiya ta yanar gizo ce ta fara daukar wannan labarin jiya Litini, bayan da ta gani a wani kundin bayani da kamfanin ya aike ma kwararru da ke wasu wurare.
Kwanan nan kamfanin na Johnson & Johnson ya kaddamar da fadadadden aikin gwaje gwajen nau’in maganinsa da ake sha sau daya. Ana gwajin ne kan mutane 60,000 a wurare sama da 200 a Amurka, da kuma kasashen waje irinsu Argentina, Brazil, Chile, Mexico da kuma Afirka Ta Kudu.
Sai dai kamfanin ya bayyana a wata takardar bayani cewa, irin wannan, abin da ya kira, “al’amari na cikas,” kamar rashin lafiya ko hatsari na daga cikin abubuwan da aka san suna iya faruwa a lokacin gwaje gwajen magani, musamman idan wadanda ake gwajin a kansu su na da yawa kamar haka. Ya ce an tsai da gwajin ne saboda kawai a yi wani dan nazari, ba wai irin dakatarwar nan ce da wata hukumar lafiya kan yi ba.
Facebook Forum