Farashin man fetur da na dizal a gidajen mai zai karu da kashi 15.4 cikin 100 da kuma kashi 25.2 cikin 100 a ranar 1 ga watan Fabrairu, yayin da man ake sayarwa masana’antu za’a kayyade shi kan 560.19 na CFA ko kuma dala (0.9317) kowace lita.
Sanar da matakin ya biyo bayan tattaunawa a kan yadda za’a daidaita tsarin sayar shi da zai dace da tashin farashin mai a duniya, a cewar sanarwar gwamnati.
An kuma bada sanarwar matakan saukaka radadin matakin na farko, ciki har da karin kashin 5.2 cikin 100 kan albashin ma’aikata da rage farashn man fitila da iskar gas da ake amfani da su a gidaje.
Gwamnati ta kuma ce za ta fara tattaunawa kan karin mafi karancin albashi.
A ranar Litinin, Hukumar IMF ta cimma yarjejeniya ta matakin ma’aikata da Kamaru kan dala miliyan 74.6 na bayar da bashi bisa ga amincewar hukumar zartarwar IMF.
Hukumomin sun shaida wa tawagar Hukumar IMF cewa, sun kudiri aniyar rage tallafin man fetur mai tsada da ake ganin ba zai dore ba a karkashin “hasashen farashin mai a duniya na wannan lokaci,” in ji Asusun.
Ya fada a ranar Litinin cewa, an yi hasashen gibin kasafin kudin Kamaru na shekarar 2022 zai yi kasa zuwa kashi 1.7 na GDP, wanda zai ci gaba da taimakawa farfadowa, da hauhawar farashin mai, da kudaden harajin da ba na mai ba, wanda ya kamata ya rage yawan kashen kudi.
Hukumar IMF ta kwashe shekaru tana kira ga Kamaru da ta rage tallafin man fetur, wanda aka kiyasta zai kai kashi 2.9 cikin 100 na GDP a shekarar 2022.
Kudin ya ninka kasafin kudin da aka warewa aikin noma sau shida, ya ninka na kiwon lafiya sau hudu kana ya haura sama da kashi uku na kasafin makamashi da ruwa, a cewar Hukumar IMF.
Reuters