A wata sanarwa da gwamnatin Kamaru ta fitar a ranar Litinin, ta bakin ministan makamashi da ruwa Gaston Eloundoun Essomba, ta sanar da cewa tuni gwamnatin kasar ta dauki matakan gaggawa na shawo kan matsalar karancin man fetur.
Sanarwar ta shafi fitar da jimillar biliyan 80 a matsayin tallafi. An riga an tattara wadannan kudaden kamar yadda Shugaban kasa Paul Biya ya bada umarni.
A cewar Ministan, ana nufin "mita cubic 28,000 na Super, 22,000 cubic meters na Diesel da 12,000 cubic meters na Jet A1". Gwamnati ta ƙayyade cewa za a fitar da waɗannan samfuran don amfanin jama’a a hankali. Gaston Eloundou Essomba ya tabbatar cewa "ƙarin juzu'i na 88,000 cubic meters na Diesel da 35,000 cubic mita na Super suna nan tafe kuma za a sauke su a cikin kwanaki masu zuwa".
A hirar shi da Muryar Amurka, Dr Dalvarice Ngoudjou masanin tattalin arziki kan wannan mataki da gwamnati ta dauka ya ce "Abin dubawa anan shi ne, gwamnatin Kamaru na kawo tallafi a fannin man fetur tun tsawon shekaru da yawa. Saboda taimaka ma al'ummar Kasar. Kadan ka duba, a ƙa'idance kudin man fetur a pompo 1013 ne na kudin CFA. Amma mai saya na biyan dala 650. Don haka abin farin ciki ne wannan mataki da gwamnati ta ɗauka. A yayin da mai yayi tsada a faɗin duniya. Yin hakan zai taimaka wa gwamnatin da kanta saboda kiyaye hauhawar kudaden sauran kayan masarufi ".
Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya koka kan tsadar tallafin man fetur da gwamnatin Kamaru ke aiwatarwa, wanda "zai yi wuya a dore a kididdigar farashin mai na duniya a halin yanzu".
A cewar IMF, tasirin hauhawar farashin mai na kasa da kasa a halin yanzu kan kasafin kudin kasar Kamaru ya yi yawa, saboda karuwar kudaden shigar man fetur ya zarce sakamakon wani gagarumin karin tallafin man fetur a fanfo da aka kiyasta ya kai kashi 2, 9% idan aka kwatanta da 0.5% a cikin 2021.