Rundunar sojojin Najeriya tace mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari kan garin Konduga ranar Lahadi amma aka fatattake su. Jami'an sojin kasar suka ce batakashin da ya dauki sa'o'i biyar sun hallaka 'yan bindidgar 72, ita kuma sojanta daya ya mutu. Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta wace ta gaskanta wannan ikirarin.
Gameda fefen vidiyo da kungiyar ta Boko Haram ta fitar jiya Litinin da ya nuna tana datse kawunan wasu 'yayanta da take yiwa zargin zama 'yan leken asiri, wani jami'in Amurka baya jin wannan sabuwar shaida ce na karuwar dangantaka tsakanin Boko Haram da kungiyar ISIS, duk da kamanni vidiyon da na ISIS data fito dasu a baya.
"Akwai kokwonto ainun, gameda kasancewar dangantaka tsakanin kungiyoyin biyu" wani jami'in Amurka wanda bai so a bayyana sunansa ba ya gayawa Muryar Amurka. Yace, in banda farfaganda ita Boko Haram ta dukufa ne kan Najeriya.
A fefen vidiyon da Boko Haram ta fitar ranar Litinin a dandalin internet, mai suna "Gamawa da 'yan leken asiri" ya nuna datse kawunan wasu mutane biyu wadanda ake yiwa zargin leken asiri. Dukkansu biyu an tilasta musu durkusawa yayinda mayakan sakai rike da dogayen wukake suka tsaya a bayansu.