WASHINGTON, DC - A wani taron tattauna kalubalen da aka yi ranar Litinin a birnin Yaoundé, hukumomin sun ce rashin tsaro, aukuwar bala''i, da rikicin kabilanci na daga cikin abubuwan da suka haddasa karancin abinci a kasar mai yawan al’uma miliyan 26.5.
Ministan noman kasar Gabriel Mbairobe ya ce ambaliyar ruwa da giwaye sun lalata daruruwan hektar gonakin noma da na kiwon kaji, sun kuma yi sanadiyar kisan shanu, tumaki, da awaki da ba a san adadinsu ba cikin wata shida da suka wuce.
Mbairobe ya kuma ce mummunan kaura da kwari da tsuntsaye suka yi sun yi sanadiyyar lalata dubban hektocin filayen noma a Kamaru, musamman kan iyakar Chadi da Najeriya. Ya ce kusan mutane 300,000 sun samu kansu cikin matsananci ko karancin abinci da ke bukatar taimakon gaggawa, haka kuma mutane miliyan 2.6 ba su da tabbacin ko za su ci abinci ko da sau daya ne a rana.
Da yake magana a birnin Yaounde ranar Litinin a lokacin taron tattauna rikicin, Mbairobe ya ce galibin farar hula da ke fuskantar barazanar karancin abinci na kuma fama da tashin farashin kayayyaki da yakin Rasha a Ukraine ya haifar.
Gwamnatin Kamaru ta dora alhakin karin kashi 15 zuwa 30 cikin 100 na farashin kayan abinci, musamman alkama, masara, dawa, da kuma shinkafa da ake yawan amfani da su a yankunan da ke bakin iyaka da Najeriya da Chadi a kan yakin.
Kasar Kamaru dai ta dogara ga Ukraine wajen shigo da kashi 60 cikin 100 na alkama. Yakin ya sa farashin buhun alkama mai nauyin kilogram 50 ya tashi daga dala 35 zuwa dala 60, adadin da gwamnatin kasar ta ce galibin talakawa ba za su iya saye ba.