Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamala Harris Ta Gana Da ‘Yan Majalisar Jihar Tennessee Da Aka Kora


Lokacin ziyarar da Kamala Harris ta kai Nashville, babban birnin Tennessee
Lokacin ziyarar da Kamala Harris ta kai Nashville, babban birnin Tennessee

Justine Jones da Justine Pearson sun yi bore ne kan neman majalisar ta dauki matakan dakile hare-haren bindiga, sai dai hanyar da suka bi wajen gabatar da korafinsu ta sabawa dokar majalisar.

Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris, ta kai ziyara jihar Tennessee da ke kudancin Amurka, inda ta caccaki ‘yan Republican da ke majalisar dokokin jihar saboda korar wasu abokanan aikinsu ‘yan Democrat biyu da suka yi daga majalisar.

Sallamar mambobin biyu na zuwa ne bayan wata zanga-zangar neman a kara tsaurara matakan mallakar bindiga da su yi a zauren majalisar.

Yayin wani jawabi da ta yi a jami’ar Fisk da asalinta ta bakaken fata ce, wacce ke birnin Nashville, Harris ta ce an kori ‘yan majalisar dokokin biyu ne saboda sun tsaya tsayin daka don a kare rayukan yara kanana, tana mai nuni da harin da ya halaka wasu dalibai a wata makaranta a Nashville a watan da ya gabata

Mataimakiyar shugaban kasar ta gana cikin sirri da ‘yan majalisar da aka kora, wato Justine Jones da Justine Perason da kuma wata ‘yar majalisar Gloria Johnson ‘yar republican da ta shiga zanga-zanga, wacce ba a kore ta ba, saboda rinjaye da ta samu da kuri'a daya.

Yayin zanga-zangar da suka yi, ‘yan Democrat uku sun doshi gaban zauren majalisar suna rera wakoki, matakin da ya take dokar majalisar na yin komai cikin tsari.

XS
SM
MD
LG