Gwamnatin Somalia ta yi tayin bada tukuici a kan shugabannin al-Shabab 11, da suka hada da babban shugaban kungiyar da ake zargi da shirya makarkashiyar kazamin harin da aka kai kasar Kenya makon da ya gabata.
Tukuicin dalar Amurka dubu dari biyu da hamsin da za’a ba duk wanda ya bada labarin da zai kaiga kama shugaban kungiyar al-Shabab Ahmed Omar Abu Ubyed. Za’a kuma bada tsakanin dala dubu dari zuwa dari da hamsin kan wadansu kusoshin kungiyar su goma.
Kakakin gwamnati Ridwan Haji Abdiwali ya shaidawa Muryar Amurka cewa, daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo, akwai Mohamed Mahamud, wanda ake zargi da kulla makarkashiyar kai hari a jami’ar Garissa ta kasar Kenya. Harin ya yi sanadin mutuwar dalibai dari da arba’in da takwas an kuma raunata wadansu da dama.