Hukumomin a kasar Kenya suna kwashe gawarwarkin dalibai da dama da yan yakin sa kan Musulmi suka kashe a wata jami'ar Garrisa domin a gane ko su wanene.
Jiya Juma'a iyalan daliban suka taru a birnin Nairobi bayan harin da aka kai jami'ar Garrisa inda aka kashe mutane dari da arba'in da takwas da kuma mahara hudu. Yan uwa sunyi layi a gaban matuwary a yayinda suke jiran suji bayani dangane da wadanda suka bace.
Kafin ketowar alfijirin ranar Alhamis yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab suka kutsa jami'ar kuma suka fara harbin fada kan mai uwa da wabi.
Shedun gani da ido sunce daga bisani 'yan bindigan sun auna Kiristoci suka saki wasu Musulmi
Sai da jami'an tsaron kasar Kenya suka shafe sa'o'i goma sha biyar suna fafatawa da yan yakin sa kan, suka kuma ceci fiye da dalibai dari biyar kafin suka harbe maharan.
Wani dan Majalisar wakilan kasar Kenya mai suna Mohammed Dahiye Duale ya fadawa sashen Samoliya nan nan Muryar Amirka cewa akalla mutane dari da arba'in da uku da aka kashe dalibau ne. Yace akwai bayanai dake nuni da cewa maharan sun fito ne daga sansanonin yan gudun hijira dake kasar Kenya.
Shugaba Barack Obama na Amirka ya baiyana bacin ransa dangane da wannan hari. Fadar shugaban Amirka ta White House tace jiya Juma'a shugaba Obama ya bugawa takwaran aikinsa na Kenya Uhuru Kenyatta wayan tarho domin yi masa ta'aziya. Ya kuma jaddada aniyarsa ko kuma shirye shiryen sa na kai ziyara kasar Kenya a watan Yuli idan Allah ya kaimu.
Hukumomin a kasar Kenya suna kwashe gawarwarkin dalibai da dama da yan yakin sa kan Musulmi suka kashe a wata jami'ar Garrisa domin a gane ko su wanene.