Farfesa Sani Fagge mafashin bakin difilomasiyya yana ganin tun farko kasashen Afirka sun yi kuskuren sa hannu amincewa da kotun duniya. Mai fashin baki kan al’amuran siyasa Farfesa Kamilu Sani Fagge yace sauran Turawan yamma ba su sakawa irin wannan yarjejeniya hannu ba.
Wannan ce ta sa duk tsiyar da suka shuga ba sa fuskantar wannan barazana. Ya kara da cewa hatta yarda da Al-Bashir din yayi na raba Sudan ta Kudu da ta Arewa yayi ne don ganin cewa zai sami sassauci daga kotun ta duniya.
YA kara da cewa karfin tattalin arziki da kuma juya kambin siyasar duniya ya dadawa Turawan na yamma karfi wajen yadda kasashen Afirka ke neman tallafi daga wajensu. Ya bada misalin da Amurka da Isra’ila game da siyasar duniya amma ba a musu wani abu.