Da yake gabatar da lacca mai taken ‘Kalu-balen Dimokaradiyya ga bangaren Shari’a a Najeriya. Mai Shari’a Gummi, ya ce “matsalar kan fara ne tun daga matakin jam’iyyun siyasa, inda ake dora ‘yan takara ba bisa ka’ida ba, ba kuma tare da bin ka’idodin dimokaradiyya ba, sai dai bisa bukatun wasu daidaikun jama’a.”
“Lamarin ko haka yake tun daga matakin mazabu har ya zuwa na tarayya, inda daga karshe al’amuran duka kan tattaru su dawo kan bangaren shari’a, domin kuwa mutane da dama da ke ganin a zalunce su, zasu garzaya kotuna domin neman adalci”.
“Daga bisani kuma, zaka ga wasu manyan masu gidaje suna barazana da katsalandan ga kotuna, lamarin da ke kawo tarnaki ga samar da adalci”.
Mai Shari’a Gummi ya zayyano misalai da dama akan yadda jam’iyyu da ‘yan siyasa suke yin karan tsaye ga tanade-tanaden tsarin mulki da ka’idodin dimokaradiyya, lamarin da ya ce ya gurgunta ci gaban kasar a dimokaradiyyance.
Ya kara da cewa har kawo yanzu ‘yan siyasa a Najeriya basu dauki darasi ba akan matsalolin da suka haifar da kifewar jamhuriya ta daya da ta biyu a can baya ba, inda kuma ya dora alhakin ga dukkan gwamnatocin da suka gabata, ciki kuwa har da gwamnati mai ci yanzu ta shugaba Buhari, duk kuwa da alkawarin da ta yi na kawo canji.
Babban bako a taron, kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jinjinawa basaraken akan laccar wacce ya ce ta zo daidai lokaci, haka kuma ta tabo muhimman al’amura a Najeriya da ya zama wajibi a sake lale a kan su, duk da yake ya musanta wani sashe na laccar.
Ya ce “ban amince da ra’ayin babban joji ba na cewa har kawo wannan gwamnati ba abin da ya canja dangane da matsaloli da ake fuskanta.”
“Kowa ya shaida irin sauyin da aka samu a dangantaka tsakanin bangaren gwamnati ta Majalisar Dokoki, haka kuma sam gwamnati mai ci yanzu ba ta yin katsalandan ga ayukan majalisa da na bangaren shari’a”.
To ko ma dai minene, in ji gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da akwai abubuwan lura a laccar. ya ce “dukkan batutuwan da laccar ta bijiro da su, sun tattaru ne akan sha’anin kyakkyawan shugabanci, kuma wajibi ne kowa ya ba da tashi himma da kwazo domin tabbatar da kyakkyawan shugabanci, tun daga kafa jam’iyyun siyasa, da nada mukamai, da bin ka’ida wajen ba da kwangiloli da dai sauransu”.
Shi ko mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, jaddadawa yayi akan muhimmancin adalci ga ci gaban kasa. ya ce “ba wani ci gaba da za’a samu a cikin kowace al’umma muddin ba zama lafiya da walwala, haka kuma ba za’a taba samun zama lafiya da kwanciyar hankali ba idan babu adalci”.
A taron na bana, kungiyar ta tsofaffin daliban ta Kwalejin Barewa, ta karrama wasu daga cikin manyan membobinta, da suka hada da Sir Abubakar Tafawa Balewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna, Malam Aminu Kano, General Murtala Muhammad da Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki da sauran wasu muhimman mutane a Najeriya.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.
Facebook Forum