Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakar Barack Obama Ta Rasu


Sarah Obama
Sarah Obama

Mama Sarah, ta yi hidimar ganin an inganta ilimin ‘ya’ya mata da marayu a ƙauyenta na Kogelo da ke Kenya.

Kakar tsohon shugaban Amurka Barack Obama ‘yar kasar Kenya Sarah Obama ta mutu, kamar yadda iyalanta su ka tabbatar a yau Litinin.

Ta rasu tana da akalla shekara 99.

Sarah Obama
Sarah Obama

“Ni da Iyalina muna jimamin rasuwar kakarmu da muke kauna, Sarah Ogwel Oyango Obama, wacce aka fi sani da “Mama Sarah” amma mu mun fi kiranta da “Dani” ko “Kaka.” Za mu yi matukar kewar ta” Obama ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Karin bayani akan:​ Sarah Obama, Barack Obama, Kisumu, da Kenya.

Mama Sarah, ta yi hidimar ganin an inganta ilimin ‘ya’ya mata da marayu a ƙauyenta na Kogelo.

Ta mutu ne da misalin karfe 4 na asuba agogon kasar yayin da ake kula da ita a asibitin koyarwa na Jaramogi Oginga Odinga da kuma Asibitin Gyara a Kisumu, birni na uku mafi girma a Kenya a yammacin kasar, a cewar ‘yarta Marsat Onyango.

“Ta mutu da safiyar yau. Muna cikin damuwa, ”Onyango ya fadawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press a waya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG