Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Caccaki Gwamnatin Trump Game Da Cutar Corona


Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama
Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama

Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama, jiya Asabar, ya yi Allah wadai da wasu daga cikin jami’an yaki da cutar corona, yana mai shaida ma daliban jami’a da ake yayewa, a wani jawabi ta kafar yanar gizo cewa wannan annobar ta nuna cewa da dama daga cikin jami’an ba su ko ma nuna cewa sun iya da al’amarin.”

Obama ya yi magana ne a shirin nan na “Show Me Your Walk, HBCU Edition,” wanda aka nuna kai tsaye ta yanar gizo na tsawon sa’o’i biyu a Jami’o’in da tun asali na bakaken fata ne a kafar You Tube, da Facebook da kuma Twitter . Jawabin nasa ya dau salo mai ban mamaki na siyasa, sannan ya tabo batutuwan wannan lokaci fiye ma da abin da ya shafi cutar corona da kuma tasirinta kan zamantakewa da tattalin arziki.

Virus Outbreak New York Daily Life
Virus Outbreak New York Daily Life

(Birnin New York kamar an share)

Virus Outbreak US Deaths
Virus Outbreak US Deaths

(Kaburburan wadanda corona ta kashe a birnin New York na Amurka)

“Fiye da duk wani abu, wannan annobar ta tona asirin ikirarin da ake yi cewa da dama daga cikin wadanda ke tafi da harkokin yaki da cutar sun san abin da suke yi,” inji shi. Ya kara da cewa, Kai da dama daga cikinsu ma ba su ko ‘yar almarar cewa abin bai fi karfin su ba.

Obama bai ambaci sunan Shugaba Donald Trump ba ko kuma na wani jami’i a matakin tarayya ko jaha.

Yayin da ya ke taya masu sauke karatun murna da kuma masu jajen irn wahalhalun da su kan fuskanta a duniyar yau, tsohon shugaban Amurka din ya dan tabo batun bindige Ahmaud Arbery, dan shekaru 25, da aka yi a watan Fabrairun yayin da ya ke guje-gujen motsa jiki a wata unguwa a Georgia.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG