Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Na Cikin Takarar Shugaban Kasa


Kakaki Aminu Waziri Tambuwal
Kakaki Aminu Waziri Tambuwal

Sabanin abun da jama'a ke zato musamman a Sokoto kakakin majalisar wakilan Najeriya ya nuna sha'awar shiga zaben shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC.

Aminu Waziri Tambuwal zai tsaya takarar shugaban kasa maimakon takarar gwamnan Sokoto kamar yadda aka yi zato.

Wannan aniyar tasa ta samu jama'ar Sokoto a bazata. Wasu ma suna tababan sahihancin aniyar.

A tunanen wasu yakamata ya tsaya takarar gwamnan Sokoto ne domin a cewarsu ya kai jihar gaba. Kowa a Sokoto ya dauka kakakin zai tsaya takarar gwamnan a jihar. Wasu na ganin da ya dakata ya ba Janaral Buhari goyon baya domin a ganinsu shi ne kadai zai iya ceto kasar daga halin da ta shiga.

Jam'iyyar APC reshen jiahr Sokoto tace bata yi mamaki ba da tsayawar kakakin takarar shugaban kasa. Tace yadda ake kiran kakakin ya tsaya takarar sanata ko gwamna haka ma 'yan Najeriya suka kirashi ya tsaya takarar shugaban kasa.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG