Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi 'Yan Siyasa Su Gujewa Maganganun da Zasu Raba Jama'a


A jihar Gombe an gargadi 'yan siyasa su gujewa maganganun da ka iya raba kawunan jama'a

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Gombe Mr. Samuel Sabulu JP yayi gargadin ne lokacin da yake karbar takardun 'yan takarar kujerar sanata na zaben 2015.

Yace su a Gombe shugabannin ne masu adalci. Suna fadawa 'yan takara su nemi zaman lafiya domin idan suna hamayya da juna domin suna neman kujera tare to idan sun soma maganaganun batanci ba za'a samu zaman lafiya ba. Kamata yayi su zama 'yanuwan juna. Duk wanda ya samu dayan kuma ya bi, ya rungumi kadara ya marawa dan'uwansa baya.

Bappa Muhammed Nafada dattijo mai shekaru 70 ya wanke Abdulkadiri Hamma Saleh daga zargin cewa shi ba dan Nafada ba ne. Yace Abdulkadiri dan Alhaji Hamma Saleh ne. Shi Alhaji Hamma Sale dan Nafada ne. Baban Hamma Saleh ma dan Nafada ne. Suna anguwar yamma. Yace abu mai kyau baya tafiya sai da suka. Yace a lokacin NPN cewa aka yi Alhaji Shehu Shagari dan Nijer ne.

Sanata Nazif Gamawa yace zai maida hankali ga batun tsaro idan yayi nasarar komawa majalisar dattawa a zabe mai zuwa. Yace kowa ya san abun da ya addabi kasar. Sha'anin tsaro ya damu kowa.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG