Yayinda ake ta shirye-shiryen zabubbukan fidda gwani na jam’iyyu da kuma babban zaben watan Fabairun shekara mai zuwa, masu sa ran takara na bullo da dabarun jan hankalin masu kada kuri’a.
Yawancin ‘yan jam’iyyar PDP musamman a arewacin Najeriya na cewa mutum ya kamata a zaba ba jam’iyya ba, don kauce wa gajiyawa da wasu suka yi na galabar jam’iyyar tun dawowar demokradiyya a aluf dari tara da cisi’in da tara. Ita kuma jam’iyyar adawa na kira da a zabi jam’iyyar don zata iya kawo sauyi a shekarar 2015.
A yankunan da aka kafa dokar ta-bachi kuma, masu sha’awar neman takara sun maida hanakali ne wajen inganta lamuran tsaro wanda shine muhimmin abu ga yawancin al’ummar yankin fiye da alkawuran shimfida tituna da samar da ruwan sha.
Da alamu neman maye gurbin wasu ‘yan majalisar dattawa da wasu gwamnoni da suka kammala wa’adi biyu ke naman yi zai yi tasiri wajen kawo ungulu da kan zabo a tsakanin jam’iyyun da abin ya shafa.
Ga waklin muryar Amurka Nasiru Adamu El- Hikaya da cikakken rahoton.