Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kais Saied Na Tunusia Ya Sake Lashe Zabe Da Gagarumin Rinjaye


Farouk Bouasker, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Tunusia (ISIE), Yayin Da Yake Sanar Da Zaben Shugaban Kasa A Babban Birnin Kasar Tunis
Farouk Bouasker, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Tunusia (ISIE), Yayin Da Yake Sanar Da Zaben Shugaban Kasa A Babban Birnin Kasar Tunis

Shugaban mai shekaru 66 da haihuwa ya fada a cikin wani jawabi a hedkwatar yakin neman zaben sa cewa, “Za mu tsarkake kasar daga dukkan masu cin hanci da rashawa da kuma mazambata.”

Shugaba Kais Saied ya samu gagarumin rinjaye a zaben kasar Tunisia a ranar Litinin, inda ya ci gaba da rike iko bayan wa’adinsa na farko, inda aka rika daure ‘yan adawa a gidan yari tare da yi wa hukumomin kasar garambawul domin kara masa iko.

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar wacce ke yankin arewacin Afirka ta ce Saied ya samu kashi 90% na kuri’un da aka kada, kwana guda bayan kammala zabe tana mai nuna cewa yana kan gaba da gagarumin rinjaye a kasar da aka fi sani a matsayin wacce ta haifi zanga -zangar juyin-juya hali ta kasashen Larabawa sama da shekaru goma.

Shugaban mai shekaru 66 da haihuwa ya fada a cikin wani jawabi a hedkwatar yakin neman zaben sa cewa, “Za mu tsarkake kasar daga dukkan masu cin hanci da rashawa da kuma mazambata.”

Ya kuma yi alkawarin kare Tunisia daga barazana ta cikin gida da kasashen waje.

Hakan ya tayar da hankulan masu sukar shugaban kasar cikin har da Farfesa Sghayer Zakraoui, malami a bangaren shari’a da ke Jami’ar Tunis, wanda ya ce siyasar Tunisia ta sake kasancewa game da “cikakken ikon mutum daya, wanda ya fifita kansa fiye da kowa kuma gasgkata kansa cewa za’a saka jari da sakon za’a samu canji a kasar.”

Zakraoui ya ce sakamakon zaben ya yi kama da na Tunisia karkashin shugaba kasar Zine El Abidine Ben Ali, wanda ya shafe sama da shekaru 20 yana mulki, kafin zama dan kama karya na farko da zanga zanga juyin juya hali ta Kasashen Larabawa ta kifar da gwamnatin sa.

Saied ya samu kuri’u ma su yawa sama da wanda Ben Ali ya samu a 2009, shekaru biyu kafin ya tsere daga kasar yayin zanga-zanga.

Abokin hamayarsa na kusa, dan kasuwa Ayachi Zammel, ya samu kashi 7.4% na kuri’un da aka kada, bayan yana zaune a gidan yari saboda a mafi yawan lokutan yakin neman zabe yayin da aka yanke masa hukunce da yawa kan laifukan da suka shafi zabe.

AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG